5 Disamba 2025 - 19:48
Source: ABNA24
Fadar Shugaban Iraki Ta Musanta Sanya Ansar Allah Da Hezbollah A Matsayin Kungiyoyin Ta'addanci

Fadar Shugaban Iraki ta musanta masaniyarta ko amincewarsu da sanya Ansarullah da Hizbullah a matsayin kungiyoyin ta'addanci. A cikin wata sanarwa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Fadar Shugaban Iraki ta musanta "Masaniyarta ko amincewa da shawarar sanya Ansarullah da Hizbullah na Lebanon a matsayin kungiyoyin ta'addanci da kuma daskarar da kadarorinsu da kudadensu".

Sanarwar ta fayyace cewa "irin wadannan shawarwari ba a aika su ga Fadar Shugaban Kasa ba," ta kara da cewa "dokokin da Majalisar Wakilai ta zartar da kuma umarnin shugaban kasa ne kawai ake aikewa da su don dubawa, amincewa, da kuma bugawa. Ba kuma a aika da shawarwarin Majalisar Ministoci, shawarwarin Kwamitin Daskarar da Asusun Ta'addanci, shawarwarin Kwamitin Yaki da tsarkake Kudade, da umarnin da wata kungiya ta bayar ga Fadar Shugaban Kasa ba".

Sanarwar ta kuma ishara da cewa "Fadar Shugaban Kasa ba ta masaniya sanin qudirin sanya Ansarullah da Hizbullah a matsayin kungiyoyin ta'addanci da kuma daskarar da kudadensu ba sai ta hanyar kafofin sada zumunta, don haka ne yayi wannan bayanin".

Your Comment

You are replying to: .
captcha